IQNA

16:41 - February 15, 2016
Lambar Labari: 3480141
A yayain Ganawar Jagora Da Shugaban Ghana Ya Ce;

Al’ummar Syria Ne Kawai Suke Da Hakkin Fayyace Makomar Kasarsu Ba Amurka Ko Turawa Ba

Bangaren siyasa, a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Ghana Dramani Mahama, jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah sayyid Ali Khamene y ace mutanen Syria ne kawai suke da hakkin fayyace makomar kasarsu.

Al’ummar Syria Ne Kawai Suke Da Hakkin Fayyace Makomar Kasarsu Ba Amurka Ko Turawa Ba

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin jagora cewa, a yammacin Lahadi ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama da ‘yan tawagarsa da suka kai masa ziyara a gidansa da ke nan birnin Tehran, inda yayin da yake ishara da siyasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kokarin karfafa alakarta da kasashen Afirka tun farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran, Jagoran ya bayyana cewar: Kasashen ‘yan mulkin mallaka dai suna adawa da kyautatuwar alakar tsakanin Iran da kasashen Afirka, kamar yadda kuma suka kasance su ne ummul aba'isin mafi yawan yakukuwa da rikice-rikicen da ke faruwa bugu da kari kan taimakon kungiyoyin ta'addanci. To amma hanyar magance dukkanin irin wadannan matsaloli ita ce samun kusaci tsakanin ‘yantattun kasashen duniya da kuma aiki tare a tsakaninsu.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar ma'abota girman kan duniya suna tabbatar da manufofinsu ne ta hanyar haifar da rikici da yake-yake a bangarori daban-daban na duniya inda ya ce: Kungiyoyin ta'addanci da suke yankinmu da kuma nahiyar Afirka, dukkanin yaran kungiyoyin leken asirin Amurka, Ingila da haramtacciyar kasar Isra'ila ne.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da maganar shugaban kasar Ghanan kan irin matsalar da kasar Siriya take fuskanta daga ayyukan ta'addanci, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce ta wace hanya wadannan ‘yan ta'dddan suke samun irin wadannan muggan makamai na zamani da kuma kudaden da suke amfani da su. Jagoran ya ci gaba da cewa: Tushen dukkanin wadannan matsaloli su ne manyan kasashen duniya ma'abota girman kai, wacce Amurka ita ce a kan gabansu, kana ita kuma haramtacciyar kasar Isra'ila ita ce tushen ashararanci.

Jagoran ya ce mahangar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da abin da ke faruwa a kasar Siriya ita ce tabbatar da sulhu da zaman lafiya a kasar yana mai cewa: Mu dai a koda yaushe kokarin mu shi ne a kawo karshen wannan rikici don al'ummar Siriya su zauna cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, kamar yadda kuma mun yi amanna da cewa babu wata kasa ta waje da za ta tsara wa al'ummar Siriya hanyar da za su bi wajen magance wannan matsalar.

Ayatullah Khamenei ya jaddada cewar: Amurkawa da Turawa ba za su iya tsara wa al'ummar Siriya abin da za su yi ba, face dai al'ummar Siriya su ne za su tsara wa kansa yadda makomarsu za ta kasance.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa hanyar magance rikicin Siriya da fada da matsaloli irin su ta'addanci da matsalar da al'ummar Palastinu suke ciki ita ce kusaci da aiki tare tsakanin ‘yantattun kasashen duniya. Jagoran ya ci gaba da cewa: Kasashen Iran da Ghana suna da hanyoyi masu yawa da za a iya amfani da su wajen karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu, don haka muna fatan wannan ziyara za ta zamanto wata dama ta karfafa irin wannan alakar.

Har ila yau kuma yayin da yake jinjinawa gwagwarmayar da wasu shugabannin Afirka suka yi wajen samar wa kasashen nahiyar da ‘yancin kansu daga wajen ‘yan mulkin mallaka, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Wadannan fitattun mutane sun daga mutumcin nahiyar Afirka a duniya.

Shi ma a nasa bangaren, shugaban kasar Ghanan John Dramani Mahama, wanda shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani yake wa jagoranci, yayi ishara da irin ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu a fagagen ilimi ya bayyana cewar maganganun Jagoran juyin juya halin Musuluncin, wasu maganganu ne da suke kwadaitarwa zuwa ga gina wata duniya ma'abociyar sulhu da zaman lafiya. Har ila yau dangane da matsalar Palastinu kuma shugaban kasar Ghanan cewa yayi: Halin da al'ummar Palastinu suke ciki wani lamari ne da ke bakanta ran dukkanin al'ummomi. A saboda haka wajibi ne a hada kai waje guda don tabbatar da hakkokin al'ummar Palastinu.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da ayyukan kungiyoyin ‘yan ta'adda a nahiyar Afirka da Yammacin Asiya da kuma jinjinawa Iran dangane da tsayin dakan da ta yi wajen fada da ayyukan ta'ddanci, shugaban kasar Ghana ya bayyana cewar: Lalle wannan siyasa ta Iran ta girmama hakkin al'ummomi na tsaya wa kansu makomarsu da kansu, wata siyasa ce da take bisa ingantacciyar turba. A saboda haka muna fatan irin kyakkyawar rawar da Iran take takawa wajen fada da ta'addanci, za ta taimaka wajen magance rikicin kasar Siriya.

Har ila yau kuma yayin da yake mika godiya da kuma jinjinawarsa dangane da irin taimakon da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take ba wa kasar Ghana, Mr. Mahama ya bayyana cewar: A madadin al'ummar Afirka ina mika godiya da kuma jinjinawarmu ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran saboda irin rawar da ta taka wajen goyon bayan kungiyoyin neman yancin kai a nahiyar Afirka musamman kungiyar fada da wariyar launin fata ta Afirka ta Kudu.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da tattaunawar da yayi da jami'an kasar Iran a yayin wannan ziyarar tasa da kuma yarjejeniyoyin aiki tare da aka sanya hannu kansu, shugaban kasar Ghanan ya bayyana cewar: Mu dai a shirye mu ke wajen karfafa alakarmu da Iran ta bangarori daban-daban.

3475642http://iqna.ir/fa/news/3475642

captcha