
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwatan cewa, Kamal Halbawi fitaccen masani kuma tsohon shugaban kungiyar Ikhwan a yankin turai dan kasar Masar ya bayyana cewa, manufar yan ta’addan Daesh na shirya gasar kur’ani ita ce jawo hankulan matasa da kanan yara zuwa gare su tare da wanke musu kwakwale.
Jawo kanan yara masu kanan shekaru zuwa ga irin wannan gasa hankoro ne na wanke kwakwalen irin wadanna yara vtare da mayar da su ‘yan ta’adda.
Masanin ya ci gaba da cewa, ba a san Daesh da wani abu na addini ba, illa tashin hankali da ta’addanci da kisan musulmi da wadanda ba musulmi ba, saboda haka babu abin da ya hada da gasar kur’ani mai tsarki.
A cikin yan kwanakin nan ne kungiyar ta Daesh ta nuna wani faifan bidiwo, wanda a cikinsa ta jagoranci wata gasa ta karatu da hardar kur’ani a garin Fallaja na kasar Iraki, inda wasu kanan yara suka halarta.
Wasu shafukan yanar gizo masu alaka da wannan kungiya ta ta’adadnci sun bayyana wanann gasa a matsayin daya daga cikin ayyukan da za su ci gaba da gudanarwa a yankunan da suke karkashin ikonsu.
Yan ta’addanc suna samun dauki da taimako daga wasu kasashen larabawa ne wadanda suka shahara wajen yada akidar kafirta musulmi tare da kiransu kafirai da jinin ya halasta.
Daga cikin ayyukan da kungiyar take aikatawa dai har da kisan mata da kanan yara da sunan jihadi a tafarkin ubangiji, sakamakon rashin sanin addini da kuma wanke kwakwalensu da aka da munanan fatawoyi marassa kan gado.