IQNA

Taron Kara Wa Juna Sani Kan Gurbatar Tunani A Masar

23:25 - February 21, 2016
Lambar Labari: 3480160
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani taron kara wa juna sani domin yaki da gurbatar tunani da kuma magance hakan a mahangar muslunci a reshen jami’ar Azahar da ke Asyut.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Albawwaba cewa, Ahmad Tayyib babban malamin Azahar shine zai jagoranci taron tare da Yasir Dasuki gwamnan Asyut, da kuma Ibrahim Hudhud shugaban jami’ar Azahar.
Usama Abdulra’uf mataimakin shugaban jami’ar Azahar reshenta na Asyut ya bayyana cewa, babbar manufar wannan taro ita ce gabatar da ra’ayoyi a mahangar addinin muslunci, domin tunkarar matsalar da ake ciki ta yaduwar gurbatccen tunani a tsakanin al’ummar musulmi.
Ya kara da cewa yin amfani da hanyoyi na yada al’adun muslunci da koyarwarsa  atsakanin musulmi tare da fadakar da su da nuna musu hakinanin koyarwar addini, shi ne babbar hanyar shawo kan wannan matasala, tare da yi wa matasa saiti kan akidarsu ta addini.
Abdulra’uf ya kara da cewa, fahimtar koyarwar addini ta hakika ita ce babban jigo na shawo kan matsalol;in gurbatar da tunani a tsakanin muslmi ta yadda za a gane cewa shi addinin muslnci da al’adunsa da kuma abubuwan da ya gadar bas u da alaka da abin da ake kokarin danganta masa na ta’addanci a duniyar yau, kuma masu yin hakan da sunan addini sun yi wa muslunci mummunar fahimta.
captcha