IQNA

Wani Limamin Wahabiyawa Ya Ci Zarafin Mabiya Darikar Shi’a

23:29 - February 21, 2016
Lambar Labari: 3480162
Bangaren kasa da kasa, masu gudanar da ayyuka a bangaren shafukan yada zumunta da kuma Youtube sun saka wani faifan bidiyo da a cikinsa limamin Makka yake cin zarafin mabiya tafarkin iyalan gidan manzo.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alalam cewa, a cikin wannn fim na bidiyo limamin wahabiyawan yana cewa kasarsa tana kokarin tabbatar da tsarin dimokradiyya ne a kasar Syria.

Haka nan kumka malamin wahabiyan mai dauke da akidar kafirta musulmi ya bayyana shi’a da kiristoci da yahudawa amatsayin abu guda, tare da yin addu’a ga ‘yan ta’adda masu kashe al’ummar musulmi a Syria da Iraki kan cewa Allah yaba su nasara kana bin da suke yi.

Wannan matsayi dai manyan sarakunan kasar ne ke nada shi, kuma yana bayyana mahangarsu da siyasarsu ne da sunan limamin wannan harami mai tsarki, inda kai tsaye yake nuna goyon baya ga ayyukan ta’addan Daesh da Jabhat Nusra, kamar yadda a cikin kwanakin nan ministan harkokin wajen kasar a zantarwarsa da jaridar Der Spiegel ta Jamus shi ma ya tabbatar da hakan.

3477234

captcha