IQNA

16:50 - February 27, 2016
Lambar Labari: 3480183

An Bude Wata Cibiyar Muslunci A Kwalejin Rocland Da Ke Jami’ar New York

Bangaren kasa da kasa, an bude wata cibiyar muslunci a cikin kwalejin Rockland da ke cikin wannan babbar jami’a ta New York domin kula da lamurra da addini.

An Bude Wata Cibiyar Muslunci A Kwalejin Rocland Da Ke Jami’ar New York

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wanann cibiya za ta rika gudanar da ayyuka da dama, da suka hada da shirya taruka kan addini da wayar da kan mutane.

Sadra Ijaz daya daga cikin wadanda suka shiga gaba domin ganin wannan shiri ya ci nasara kamar yadda aka shirya, ta bayyana gamsuwarta matuka da hakan.

Bayanin ya ci gaba da musulmi ne za su jagoranci ragamar gudanar da ayyykan wannan cibiya da ke cikin kwalejin, musamman ma wadanda suka danganci wayar da kai a tsakanin mutanen kasar.

Azim Faruki daya daga cikin manyna jami’ai na jami’ar da suke gudanar da ayyukansu awannan jami’a kuma, ya bayyana jin dadinsa matuka, kasantuwarsa muusmi kuma mai matukar fatan ganin an samu ci gaba irin wannan.

Ya ce wannan cibiya a halin yanzu tana da mambobi 200 dukakninsu kuma suna gudanar da ayyukansu na yada al’adu a wannan kwaleji.

Haka nan kuma ya ce akwai matasa yahudawa da suke da kyakyawar dangantaka da musulmi da suke son su shiga ciki domin sanin addinin muslunci da kuma wayar da kan yansu.

Daga karshe dai wannan cibiya tana da shirye-shirye da dama da take da nufin aiwatarwa a cikin wannan kwaleji na bunkasa addinin muslunci da wayar da kan jama’a a kansa.

3478662

captcha