IQNA

23:39 - March 02, 2016
Lambar Labari: 3480195

Masu Fasaha Sun Kayata Bangaye Da Ayoyin Kur’ani A Bahrain

Bangaren kasa da kasa, masu fasaha a Bahrain sun gudanar da wani aiki na fasaharsu a kasar ta hanyar kayata bangaye da zane mai dauke da ayoyin kur’ani da hadisan ma’aiki.

Masu Fasaha Sun Kayata Bangaye Da Ayoyin Kur’ani A Bahrain

Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alwasat cewa, wasu daga cikin masu fasaha akasar Bahrain sun gudanar da wani aiki na fasaharsu ta hanyar kayata bangaye da allunan bakin titi da zane mai dauke da ayoyin kur’ani da hadisan ma’aiki domin fadakarwa.

Wannan dai yana daga cikin hanyoyin da masu fasahar ke ganin za su iya bayar da gudunmawarsu wajen fadakar da al’umma da kma ilmantarsu ta hanyar tunatarsu fadar ubangiji da manzonsa, domin gyaran zamantakewar al’umma.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan lamari ya samu karbuwa matuka daga jama’a inda kowa yake nuna farin cikinsa da hakan, kamar yadda kuma wasu daga cikin masu zanen sun rika hadawa da baitocin wakoki masu koyar da darussa na rayuwa.

Masu ilmimin fasahar rubtun dai suna amfani da hanyoyin zane-zane na zamani, ta yadda hakan zai zama mai jan hankali matuka ga jama’a masu wucewa, ta yadda za su tsaya su karanta a bin da aka rubuta da kuma fahimtar abin da ake nufi cikin sauki domin ilmantuwa.

Ana sa ran lamarin ya samu karbuwa fiye da kowane lokaci a baya, ganin yadda jama’a suka gamsu da hakan fiye da kowane lokaci da ake gudanar da wannan aiki na fasaha a kasar.

3479736

captcha