
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, Muhammad Isma’il, na hannun damar Saif Islam dan tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Libya ya bayyana a zantawarsu da jaridar Times cewa, an kashe Imam Musa Sadr bayan da suka yi cacar baki tare da Gaddafi kana bin da ya shafi gwagwarmayar Lebanon.
Isma’il ya kara da cewa babu hannun ko daya daga cikin iyalan Gaddafia cikin kisan Imam Musa Sadr, amma na hannun damar Gaddfi ne suka aiwatar da wannan kisa, musamman ma manyan jami’an tsaronsa da kuma na leken asiri.
Ya ce a wancan lokacin mun yi karyar cewa Imam Musa Sadr ya bar kasar Libya zuwa kasar Italia, amma wannn Magana ba ta da tushe, domin kuwa an kasha an kuma jefa gawarsa a cikin ruwa.
Har yanzu dai ba gasgata wannan bayani kan shahadar Iamm musa Sadr ba tare da wadanda suke tare da a shi a lokacin da suka yi wanann tafiya.
An dai haifi Imam musa Sadr a birnin Qom na kasar Iran, kuma shi ne babban jagora na mabiya mazhabar shi’a a kasar Lebanon, tun daga ranar 31 ga watan Agustan 1978 aka ga Imam Musa Sadr tare da abokan tafiyarsa Sheikh Muhammad Yakub, da Abbas Badruddin a birnin Tripoli a cikin motar alfarma, har yanzu babu duriyarsu.
Tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Mu’amma Gaddafi ya ce Imam musa Sadr tare da abokan tafiyarsa sun tafi Italia acikin jirgi mai lamba 881, amma wannan labari daga bisani ya tabbata karya ce.