Bangaren kasa da kasa, Juko Widodo shugaban kasar Indonesia ya fadi a gaban taron kasashen musulmi cewa, hakurin kasashen duniya kan ayyukan ta’addancin Isra’ila ya zo karshe.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almisri Yaum cewa, Juko Widodo shugaban kasar Indonesia ya fadi a gaban taron kasashen musulmi karo na 50 cewa ci gaba da mamaye yankunan palastinawa da Isra’ila take yi ya kawo am al’ummomin duniya ga wuya.
Ya ci gaba da cewa ko shakka bubabu abin haramtacciyar kasar Isra’ila take yi ya zama wani babban bal’I da ya addabi kashen duniya,a akan haka ya zama wajibi a tunkari wanann matsala domin kawo kasrshenta baki daya.
An fara gudanar da taron ne mai take Palastinu da quds a karo na hamsin a birnin Jakarta fadar mulkin kasar ta Indonesia tare da halartar wasu daga cikin wakilan kasashen muuslmi.
Daga cikin kasashen ad suka halarta baya ga Indonesia akwai Pakistan, Sudan, Palastinu, Qatar, Saudiyyah, Iran, Turkiya Afghanistan Bahrain, Saliyo, da dai sauransu duk suna daga cikin masu halartar wannan zaman taro na kasashen musulmi, wanda shi kan kansa Iyad madani babban sakataren kungiyar yake halarta.
Kafin wannan lokacin dai an sanar da cewa shugaban kasar Masar Abdulfattah Sisi zai halarci taron, amma daga bisani kuma an sanar cewa ministan harkokin weajen kasar ne zai wakilce shi wajen karabar ragamar shugabancin kungiyar.
Kasashen 49 daga cikin kasashe 57 mambobin kungiyar ne suka sanar da cewa za su halarta.
A wannan zama dai shugaban palastinawa ya bayyana cewa halin da ake cikia halin yanzu a palastinu yay i muni matuka.