IQNA

Sheikhul Azhar Ya Yi Kira Zuwa Ga Na Hadin Kai Tsakanin Sunna Da Shi'a

23:49 - March 09, 2016
Lambar Labari: 3480215
Bangaren kasa da kasa, babban malamin cibiyar Azahar ya yi kira zuwa ga gudanar da zama tsakanin malamai na sunna da kuma mazhabar shi’a

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na tashar talabijin ta Umma Al-ikbariyya ya habarta cewa, a ganawar da babban malamin cibiyar Azahar Sheikh Ahmad Tayyib ya yi jiya tare da shugaban kasar Iraki Fu'ad Ma'asum a birnin Alkahira ya bayyana cewa, ya zama wajibi malamai su gudanar da zama domin shawo kan matsalar da ake neman haddasa a tsakanin al'ummar musulmi.

Sheikh Ahmad tayyib ya ce cibiyar Azahar a matsayinta na cibiyar musulunci ta malaman sunna mafi girma a duniya, za ta yi iyakacin kokarinta domin ganin an gudanar da wanann zama, tare da kara tabbatar da cewa musulmi shi'a da suna dukakninsu 'yan uwan juna ne, banbancin fahimta ba dalili ba ne da zai sanya wani bangaren musulmi ya kafirta wani bangare.

Sheikh Ahmad Tayyeed ya kara da cewa akwai bukatar hadin kai tsakanin musulmi kuma malaman manya manyan mazhabobin ne yakamta su jagoranci lamarin. Sheikh Tayyeeb ya bayyana goyon bayansa ga mutanen kasar Iraqi a kokarin da suke na yaki da yan ta'adda wadanda suke son raba kan al-ummar musulmi.

Shima a na shi bangaren shugaban kasar Iraqi ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta haka kai da kasar Masar don cimma manufofi masu amfanar kasashen biyu.

3481937

captcha