IQNA

22:45 - March 11, 2016
Lambar Labari: 3480221

Kungiyoyin Musulmi A Jamus Na Kokarin Samar Da Hanyoyin Taimakon Yan Gudun Hijira

Bangaren kasa da kasa, kungiyoyin mabiya addinin muslunci a kasar Jamus suna kokarin ganin sun samar da hanyoyi na taimakon yan gudun hijira da suke isa kasar.

Kungiyoyin Musulmi A Jamus Na Kokarin Samar Da Hanyoyin Taimakon Yan Gudun Hijira

Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Newsarchy cewa, fiye da mutane miliya daya ne suka isa kasar Jamus a cikin shekarar da ta gabata.

Kungiyoyin musulmin sun ce halin da yan gudun hijirar suke ciki wadanda akasarinsu mabiya addinin muslunci daga kasashen larabawa ya munana matukam a kan haka ya zama wajibi a taimnaka musu.

Nurhan Suwaikan shugaban cibiyar musulmi masu taimaka yan gudun hijira ya bayyana cewa, hakika suna fuskantar babar barazana a aikin nasu, domin kuwa a kowace rana adadin na masu gudun hijira karuwa yake, kuma abin da suke da shi baya isa su taimaka kamar yadda ya kamata.

A nata bangaren hukumar 'yan sandar bincike kan manyan laifuka a kasar Jumus ta sanar da karuwar kai hari a Sansanin 'yan gudun hijra a kasar.

Bisa rahoton da hukumar 'yan sanda mai bincike kan manyan laifuwa ta gabatar a cikin wannan shekara ta dubu biyu da sha shida an kaiwa 'yan gudun hijrar hari sau dari biyu da da sh a bakwai, wato akalla ko wata rana ana kai hari so uku a sansanin 'yan gudun hijrar.

Daga cikin wannan adadi, hari ashirin da shida an sanya wuta ne ko kuma tayar da wasu ababen fashewa a sansanin 'yan gudun hijrar.

Ana zargin masu tsatsauran ra'ayi na kin jinin baki da kai harin har so dari biyu da biyu.

Har ila yau sanarwar ta ce daga cikin wannan adadi da ta gabatar akwai mumanan har da aka kai har arbain da takwas.

A shekarar da ta gabata ma kimanin hare-hare dubu daya aka kai sansanin 'yan gudun hijrar a kasar Jamus.

3482512

captcha