IQNA

23:32 - March 19, 2016
Lambar Labari: 3480246

An Zabi Animation Na Ayoyin Kur’ani A Kyautar Fim A Bahrain

Bangaren kasa da kasa, Animation wani shiri ne na zane-zanen masu motsi da ake nunawa da ke bayani kan kissoshin kur’ani wanda ya lashe kyautar fina-finai ta kasar.

An Zabi Animation Na Ayoyin Kur’ani A Kyautar Fim A Bahrain

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bawwab Al-fajr cewa, wannan shiri an kwashe kimanbin shekaru goma sha hudu a ana gudanar da shi, wanda Yahya Fakhrani da Ahmad Bahjat suke gudanarwa, wanda kuma ya samu karbuwa matka.

Yahya Fkhrani baya ga gabatar da wannan shiri ta hanyar zane, yana kuma karanto kissoshin da ke kur’ani mai tsarki.

Wannan Animation ana gudanar da shi ne da nufin isar da sako na kissoshin da suke cikin kur’ani mai tsarki, kuma suna yin tasiri matuka domin wadanda aka yi su domin wato kanan yara, duk kwa da cewa hatta manya suna kallo a kasar ta Bahrain dama sauran kasashen larabawan yankin tekun fasha.

3484192

captcha