IQNA

23:09 - March 22, 2016
Lambar Labari: 3480254
Bangaren kasa da kasa, Atka da Marwa Samara yan uwan juna ne biyu da suke zaune a Amurka da suke kokarin ganin sun fito da kkyakkyawar surar hijabin muslunci ta hanyar Istigram The Samaras.

Bangaren kasa da kasa, Atka da Marwa Samara yan uwan juna ne biyu da suke zaune a Amurka da suke kokarin ganin sun fito da kkyakkyawar surar hijabin muslunci ta hanyar Istigram The Samaras.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na WUWM cewa, wannan shafi ya samu magoya baya da suka kai dubu 20 dagga sassa na kasar.

Duk da cewa kawayensu daga cikin Amurka ko dai mawaka ne ko kuma masu wasan kwaikwayo, amma duk da hakan wadannan yan mata biyu sun rike koyarwa ta saka hijabin mslunci a cikin kowane irin yanayi suka samu kansu a cikin kasar.

Suna cewa duk yake saka hijabin muslunci a kasar Amurka ba a bu ne mai sauki ba, amma dai duk da haka suna yin iyakacin kokarinsu domin ganin sun safke wannan nauyin da yake a kansu.

Wannan ne ma ya sanya suka yi amfani da hanyoyi na zamani domin nuna wasu daga cikin nauoin hijabi masu sauki sakawa ga mata, domin ganin an rage irin matsalar da ake fuskanta sakamakon saka hijabin, inda suka yi shi mai sauki marassa daukar hankali a tsakanin jama’a.

3484358

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: