IQNA

23:36 - March 23, 2016
Lambar Labari: 3480256
Bangaren kasa da kasa, an kai batun kisan mabiya mazhabar shi’a mabiya sheikh Zakzaki a Najeriya agaban koun manyan laifuka ta duniya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin Alalam cewa, kwanaki dari bayan kisan kare dangi da sojoji suka yi a Zariya, Harka Islamiyya ta shigar da gwamnati Tarayya da sojoji kara kotun duniya da ke birnin Hague bisa kisan sama da mutane dubu da sojoji suka yi a Zariya.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Musulunci da ke birnin landan ce ta shigar da karar da hadin gwiwar Harkar Musulunci suna neman a yi adalci kan kasin kiyashin da sojoji suka yi.

Mutane 217 ne aka tabbatar ad sun mutu, wasu kimanin 219 sun jikkata, yayin da wasu kimanin 482 suka bata bat.

A taron manema labarai da Harkar Musulunci ta kira ran Litinin a Kaduna, ta bayyana matukar damuwa a kan rashin bai wa Lauyoyi damar ganin Jagoran Harkar Musulunci, Shekh Ibrahim Zakzaky da gwamanti ta yi.

Harkar Musulunci ta bukaci gwamnatin Tarayya ta yi gaggawar sakin dukkan 'yan uwan da take tsare da su tsawon watanni uku ba tare da sun aikata laifin komai ba.

3484401

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: