IQNA

23:46 - March 24, 2016
Lambar Labari: 3480259
Bangaren kasa da kasa, wasu mutane sun kai hari kan babban masallacin birnin Madrid na kasar Spain tare da kone shi.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na an7a.com cewa, jami’an yan sanda na birnin sun tabbatar da kai harin, tare da daukar kwaran matakai na bincike kan lamarin.

Wannan hari dai ya zo ne bayan faruwar abin da aka yi abirnin Brussels na kasar Belgium, inda aka kai harin ta’addanci, wanda wasu musulmi masu akidar kafirta jama’a suka kai.

Bangarori daban-daban a kasar ta Spain sun yi Allawadai da wannan hari da aka kai kan babban masallacin musulmi, tare da bayyana hakan ba zai taba zama dalilin cutar da musulmin da ba su ba su gani ba.

A nata bangaren babbar kungiyar msulmi a kasar ta bayyana cewa, mafi yawan hare-haren ta’addancin da ake kaiwa cwanda masu akidar kafirta musulmi suke kaiwa, musulmi ne suke zama wadanda abin abin ya fishafa.

Daga karshe an kirayi mahukunta a kasar ad su dauki matakan kare muslmi da dukiyoyinsu da kuma raykansu, gami da wuraren ibadarsu da kuma cibiyoyinsu na addini.

3484429

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: