IQNA

Jagoran Juyin Juya Hali ya Ce:

Yanzu Lokacin Makami Mai Linzami Ne Kuma Lokacin Diplomasiyya

16:55 - April 01, 2016
Lambar Labari: 3480281
Bangaren siyasa, a lokacin da yake ganawa da wasu daga cikin mawaka da masu bege ga manzo iyalan gidansa, jagoran juyin jya halin muslunci ya bayyana cewa, yanzu lokaci ne wanda dukaknin bangarori biyu suke aiki tare bangaren nuna karfin kare kai da kuma diplomasiyya.
Kamfanin dillanicn labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na jagora cewa, a safiyar yau Laraba ce, wadda ta yi daidai da ranar haihuwar Nana Fatima, amincin Allah ya tabbata a gare ta, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da gungun mawaka da masu yabon Ahlulbaiti (a.s) inda ya bayyana cewar bayanin hakikanin rayuwar Ahlulbaiti (a.s) wani lamari ne da zai kara irin tasirin da mawaka da masu yabon suke da shi. Haka nan kuma yayin da yake ishara da kokarin da makiya suke yi ba dare ba rana wajen fada da al'ummar Iran da kuma tsarin Musulunci na kasar, Jagoran ya bayyana cewar: Bisa la'akari da irin yanayi mai sarkakiya da ake ciki a halin yanzu, wajibi ne a yi amfani da dukkanin karfi na siyasa, tattalin arziki, zamantakewa da kariya wajen kara karfafa matsayin da Iran take da shi.

Yayin da yake isar da sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwar Nana Fatima (a.s), Jagoran ya bayyana wake da kuma yabon Ahlulbaiti (a.s) a matsayin wani abin alfahari inda ya ce: Waken yabo da dukkanin bangarorinsa, daya ne daga cikin siffofin da al'ummar Shi'a suke kebanta da su. A saboda haka yana da kyau daliban jami'oi da cibiyoyin ilimi da bincike su samo hanyoyin fadada wannan aikin.

Haka nan yayin da yake magana kan matsayi da daukakar Nana Fatima al-Zahra (a.s), Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar fahimta da kuma bayanin matsayi mai girma da Sayyida Zahra (a.s) take da shi wani lamari ne ba mai yiyuwa ba inda yace: To amma duk da hakan, akwai wasu batutuwa masu yawa cikin rayuwa da dabi'unta da za a iya bayaninsu sannan kuma su zamanto mana darasi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana kasantuwar Fatima al-Zahra (a.s) ‘yar Manzon Allah kana kuma matar Waliyin Allah (Imam Ali) wani lamari ne da ke nuni da irin girman matsayin da take da shi inda ya ce: Tarbiyyar shugabannin matasan ‘yan Aljanna guda biyu, haka nan da tsarki na ruhi da kuma rayuwa bugu da kari kan tsarki na zuciya suna daga cikin siffofin da ta kebanta da su wadanda za su iya taka rawa wajen kyautata rayuwa ta daidaiku da zamantakewa ta bil'adama.

Haka nan yayin da yake kiran mawaka da maso yabon Ahlulbaitin zuwa ga sanya wadannan abubuwan cikin wakokin da suke tsarawa, Jagoran ya bayyana cewar: Ambato (zikiri) wani lamari ne da ke samar da kauna da kuma haske na zuciya, to amma hakan dai ba ya wadatarwa. Wajibi ne a duk wani mimbari a yi bayanin darussan da suke cikin rayuwar Imamai (a.s) cikin hikima da kwarewa wanda hakan zai share fagen mika musu wuya da kuma riko da tafarkinsu a aikace.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana kula da kuma ba da muhimmnaci ga lamurran yau da kullum cikin wakokin masu yabon Ahlulbaitin a matsayin wani lamari da ya zama wajibi inda ya ce: Babu wani kokari da tsarin girman kan duniya wanda ya dogara bisa ‘amfani da karfi da kuma tilasci na siyasa, tattalin arziki, al'adu da kuma karfin soji, bai yi ba wajen cutar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma al'ummar Iran. Bai kamata a rufe ido kan wannan lamarin ba.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin amfani da duk wata hanya ta da da kuma ta zamani da makiya suka yi wajen fada da Iran, Jagoran jhhm cewa yayi: Wadannan mutanen suna amfani da hanyoyin irin su tattaunawa, ciniki, takunkumi, barazanar soji da sauran hanyoyi na daban don cimma manufofinsu. A saboda haka wajibi ne mu din nan mu ma mu yi amfani da dukkanin fagage da kuma karfinmu wajen karfafa garkuwarmu.

Jagoran ya bayyana karfin soji a matsayin babban abin da ma'abota girman kan suka dogara da shi wajen fada da al'ummar Iran. A saboda haka sai Jagoran ya gabatar da wata tambaya cewa: A irin wannan yanayi da rikici da duniya take ciki, idan da a ce al'ummar Iran za ta yi riko da tafarkin tattaunawa da musayen kayan kasuwanci kai hatta ma ilimi, amma ba ta da karfi na kare kai, shin gwamnatocin kananan kasashe ma ba za su share wa kansu fagen yin barazana ga al'ummar Iran?

Haka nan kuma yayin da yake kakkausar suka ga masu sukar shirin makamai masu linzamin Iran din da bayyana cewar a halin yanzu tattaunawa ita ce kawai hanyar magance matsaloli, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Ko yaunzu ma wadannan makamai masu linzamin suna da ranar su, idan kuwa ba haka ba, cikin sauki za su danne hakkokin al'ummar Iran.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Idan har suna fadin hakan bisa gafala da rashin sani ne, to hakan wani lamari ne na daban. To amma idan har da sani aka fada, to hakan ha'inci ne.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar gwajin makamai masu linzami da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran suka yi a kwanakin baya wani lamari ne da ya faranta ran al'ummomin da suke kyamar Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila, to sai dai babu yadda za su yi ne.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Makiyanmu a kullum suna ci gaba da kara karfafa irin karfi na soji da makamai masu linzami da suke da shi ne; to amma da wani dalili za su ce zamanin amfanin makamai masu linzami ya kare?

Ayatullah Khamenei ya bayyana irin wadannan maganganu da cewa maganganu ne da suka yi kama da na wasu daga cikin jami'an tsohuwar gwamnatin rikon kwarya ta Iran wadanda a farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci suna cewa mu mayar wa Amurka da jiragen yakin samfurin F-14 da muka saya, don kuwa babu wani amfani da za su yi mana.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: A wancan lokacin mun tsaya kyam da kuma tona musu asiri. Ba a jima ba kuwa a lokacin da Saddam ya kawo wa Iran hari, a lokacin aka gane irin tsananin bukatar da muke da shi ga wadannan makamai na kariya.

Haka nan kuma yayin da yake sake jaddada maganar amincewarsa da batun tattaunawa da amfani da hanyoyi na diplomasiyya wajen magance matsalar nukiliya in ban da ‘yan wasu abubuwan da ya ki amincewa da su, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: Bai kamata su dinga yada farfaganda tamkar ina adawa da tattaunawa ne. Ni dai abin da nake cewa shi ne wajibi ne a yi taka tsantsan sannan kuma a tsaya kyam yayin tattaunawar, don kada a yaudare mu.

Dangane da batun tattalin arzikin dogaro da kai kuwa da Iran ta sa a gaba a hankalin yanzu, Jagoran cewa yayi: Ci gaba da maimaita kalma da kuma take guda wani lamari ne mai gajiyarwa. A saboda haka a halin yanzu dai lokaci ne na aiki a kas da nufin karfafa yanayin tattalin arzikin kasar nan da kuma kyautata rayuwar al'umma.

A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi mawaka da masu yabon Ahlulbaiti (a.s) din da su ba da himma wajen fada da kokarin da makiya suke yi wajen raunana akidun matasa inda ya ce: Ana ta kokari wajen raunana imanin matasa dangane da addinin Musulunci da kuma koyarwar wannan tsari na Musulunci, kai har ma suna kokarin nuna cewa Jamhuriyar Musulunci ba abu ne da zai ci gaba da wanzuwa ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Koda yake shekaru 37 kenan makiya ta hanyoyi da makirce-makirce daban-daban suke nuna cewa tsarin Musulunci dai ba wani abu ne da zai dawwama ba. To amma wannan tsari da al'ummar Iran suka zama ya tashi daga tsiro a farkon nasarar juyin juya halin Musulunci zuwa ga wata bishiya tsayayyiya. Hakan kuwa lamari ne dake nuni da irin kwarewa da kuma aiki tukuru da ake da shi ne a cikin tsarin Musulunci kuma a kowace rana yana ci gaba da karfafuwa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar makomar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dai wata makoma ce mai kyau.

3484960

captcha