Ministan harkokin cikin gidan kasar Jamus Thomas de Maizière ya bayyana muslunci a matsayin addinin sulhu da rahma.
Shafin yada labarai na Akhbar Khalij
ya bayar da rahoton cewa, Ministan harkokin cikin gidan kasar Jamus Thomas de
Maizière ya bayyana hakan ne a jiya,a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a
wata cibiyar muslunci ta Azhar da ke birnin Alkahira a kasar Masar.
Ya ce a yau duniya na bukatar sulhu da zaman lafiya da fahimtar juna da yafiya
a tsakanin dukkanin al'ummomi da addinai, ya ce kasarsa na gormama musulmi da
addinin msulunci.
Thomas de Maizière ya ce yana son ya yi amfani da wannan damar domin ya shedawa
dukkanin al'ummomin duniya cewa muslunci ba addinin ta'addanci ba ne kamar
yadda wasu suka dauka.
Ministan na Jamus ya ce abin nufi da fahimtar juna shi ne girmama ra'ayi da
akida, kuma kowa rike abin da ya fahimta ba tare da tilasta daya bangaren a kan
fahimtarsa ko akidarsa ba, amma a rayu tare a yi komai tare wanda ya hada ku a
matsayin 'yan adam ko yan kasa, a bangaren sddini kuma ko akida kowa ya yi nasa
a cikin 'yanci.
Ya kara da cewa kyamar musulmi a nahiyar turai ta karu ne sakamakon ayyukan
ta'addanci da wasu ke yi kuma suna danganta kansu da muslunci, saboda mutanen
turai ba su da masaniya a kan cewa abin da 'yan ta'adda suke ba muslunci ba ne.