IQNA

Masu Ra’ayin Yan Mazana Jiya A Birtaniya Na Kara Yada Kyamar Musulmi

23:36 - April 02, 2016
Lambar Labari: 3480285
Bangaren kasa da kasa, masu tsatsauran ra’ayin yan mazana jiya a tsakanin yan siyasa a kasar Birtaniya suna kara yada kyamar musulmi a kasar.

Kamfanin dillanicin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anadolu Agency cewa, wasu daga cikin masu tsatsauran ra’ayin yan mazana jiya a tsakanin yan siyasa da kungiyoyin yan daba a Birtaniya suna kara yada kyamar musulmi tun bayan kai harin Brussels da paris.

Victoria Britian wata yar jarida kuma marubuciya a kasar ta bayyana cewa, wannan lamari yana faruwa kuma ana ganinsa a fili.

Ta ci gaba da cewa bata tsammanin wadannan kungiyoyi su yi wani babban tasiri wajen saka mutanen kasar su kyamaci musulmi, domin kuwa kansu kngiyoyi ne da mutane suke kyamar su.

Masu wanann ra’ayi suna ganin cewa duk da kasantuwar irin wadannan kungiyoyi a kasar ta birtaniya kadan ne kamar irin su All Britania, amma kuma suna yin iyakacin kokarinsu domin yin tasiri.

Iman Abu Ata daya daga cikin jagororin kungiyar Tell mama ta bayyana cewa, wadannan kngiyoyi masu kyamar msuulmi, ba musulmime kawai suke wulakantawa ba, har ma da sauran al’ummomin kasar.

Masu kyayya da msuulmi a cikin kasashen trai dai suna fakewa ne da ayyukan ta’addanci da masu akidar kafirta musulmi ske aikatawa a cikin kasashen, inda suke danganta hakan da musulunci suna cutar da msuulmi da kuma yada kiyayya a kansu.

3485125

captcha