IQNA

Babban Baje Kolin Kur’ani A Kasar Birtaniya

23:51 - April 05, 2016
Lambar Labari: 3480293
Bangaren kasa da kasam an fara gudanar da wani babban baje kolin kur’ani mai tsarki a kasar Birtaniya a dakin ajiye kayan tarihi na Bakingham a garin Elezibry.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya naklato daga shafin sadarwa na Islam Today cewa, masu gudanar da wannan baje koli sun yi iamnin cewa shi ne irinsa mafi girma da aka taba gudanarwa akasar.

Wannan baje kolin kur’ani mai tsarki dai ya hada da kwafin kur’ani na daruruwan shekaru da aka rubuta da hannu da kuma na zamani wadanda aka buga su da injin.

A gefen wannan baje koli akwai wasu shiry-shirye da suka kai kimanin 100 da ake gudanarwa a wurin da suka shafi wayar da kai kan muslunci.

Ana gudanar ad shirin ne tare da hadin gwiwa da cibiyoyin addini da na al’adu da kuma kawamitocin wasu masallatai da kuma dakunan karatu na musulmin kasar.

Daga cikin muhimamn abubuwan da ake gudanarwa kuwa baya ga baje kolin kur’ani da abubuwan da suka dangance shi, akwai wakoki, adabi, zane, da kuma kida irin na muslunci da sauran abubuwan da suke bayyana al’adu a cikin addini.

Baya ga birnin na Bakingham, ana gudanar da wani baje kolin makamncin hakan a birnin Landan wanda shi ne fadar mulkin kasar, wanda shi ma yake samun halartar mutane daga addinai daban-daban.

Richard Depeir shi ne babban daraktan babban dakin kayan tarihi na Bakingham ya bayyana cewa, wanann baje koli na kur’ani yana daya daga manyan baje kolin da ya taba a gani a wannan wuri.

3485713

captcha