Bangaren kasa da kasa, babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya bayyana cewa mafi yawan mutaen da suka rasa rayukansu sakamakon ayyukan ta’addaci msuulmi ne.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya
habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na Anatoli cewa, babban sakataren
majalisar dinkin duniya ya bayyana hakan ne a taro kan yaki da ta’addanci.
Ban Ki Moon ya bayyana cewa babu shakku kan wannan batu kan cewa mafi yawan mutaen da suka rasa rayukansu sakamakon ayyukan ta’addaci a duniya mabiya addinin muslunci ne.
Ya ci gaba da cewa irin barazanar da duniya take fuskanta a halin yanzu daga yan ta’adda, za a iya fahimtar cewa wannan barazana bata bar kowa ba, musulmi da wand aba musulmi ba, domin kuwa yan ta’adda ba su da addini.
Haka nan kuma ya yi tsokaci dangane da batun yiwuwar yan ta’addan su iya samun makamai masu guba, wanda kuma tabbas za su yi amfani da su kan al’ummomin duniya, wanda kuma hakan yan atattare da gagarumin hadari ga zaman lafiyar duniya baki daya.
A kan hakan y ace ya zama akan dukkanin kasashen duniya su hada karfi da karfe domin fuskantar wannan barazana da kuma sanin hanyoyin shawo kanta cikin gagagwa.
Kamar yadda kuma yay aba da irin kokarin da kasashen duniya da dama suke yi kan hakan, inda y ace yana da kyaua kara irin wannan kokari na hadiun gwiwa atsakanin dukkanin kasashe.
Ban Ki Moon ya bayyana hakan ne a gaban taron kasa da kasa a birnin Geneva kan barazanar ta’addanci, tare da halartar kasashe 32 na duniya.