IQNA

Tantawi Ya Nuna Rashin Jin Dadi Kan Kin Gayyatar Iran A Gasar Masar

20:28 - April 12, 2016
Lambar Labari: 3480316
Sheikh Muhammad Abdulwahab Tantawi daya daga cikin manyan makarantar kur’ani kuma alkali na kasa da kasa dan asalin kasar Masar azanatawa da Iqna, ya nuna damuwa kan yadda mahukuntan kasar Masar suka ki gayyatar Iran zuwa gasar kur’ani ta duniya akasar.

Shehin malamin ya ce batun gasar karatun kur’anii lamari ne wand aba shi da wata alaka da siyasa, Magana ce da ta shafi kasashen tafuskar addini kawai ba siyasa.

Ya kara da cewa kowa ya san cewa makarantan kur’ani na kasashen duniya daban-daban ne suka halartar gasar kur’ani ta kasa da ake gudanarwa Masar, da hakan ya hada har da kasashen da ban a musulmi ba, idan har za a gayyaci makaranta daga wasu kasashen da ban a musulmi ba, mene ne dailin kin gayyatar Iran? Da wasu kasashe.

Haka nan kuma kan batun yadda ake nuna wariya da banbanci kan batun akida a cikin gasar kur’ani, ya ce wannan babban kure ne, domin kuwa ana maganar muslunci ne da kur’ani ba akida acikin muslunci ba, kur’ani ya hada dkkanin muslmi da kuma dukkanin akidu da mabiyansu a cikin musulmi.

Gasar kur’ani ta kasar Masar dai na daga cikin irinta masu muhimamnci da ake gudanarwa a duniya, wadda ke samun halartar makaranta da mahardata daga sdassa na kasashen musulmin duniya.

Inda babbar cibiyar da ke kula da harkokin kur’ani karkashin kulawar ma’akatar kula da harkokin addini ta kasar kan dauki nauyin shiryawa da kuma gudanarwa.

Wakilan kasashen Iran, Qatar da kuma Turkiya ne dai ba a gayyata a wajen wannan gas aba kamar yadda aka yi a shekarar da ta gabata, wanda kuma hakan ya zama babbana bin kunya ga mahukuntan na Masar.

3487651

captcha