
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ala’alam cewa, babbar majalisar malan addinin muslnci ta kasar Lebanon ta bayyana zaman da aka gudanar a na kasashen muslmi a birnin Istanbul na kasar Turkiya da cewa ya kara girman Baraka atsakanin kasashen musulmi.
Bayanin da kungiyar ta fitar ya yi ishara da cewa hakika abin da ya faru yana da matkar hadari, ta yadda a halin yanzu musulmi ba su da wani kudiri a hannunsu sai abin da aka shirya musu daga waje.
Hak nan kma sun kira da a gaggauta kawo karshen wannan yunkuri na taba kan al’ummar msuulmi ta hanyar sukar wasu daga manyan kasashen musumi da kuma bayyana su a matsayin masu daukar nauyin ta’addanci saboda dalilai na siyasa.
Kamar yadda kuma ska bukaci a kawo karshen harin da gidan sarautar Saud ke kaddamarwa kan al’ummar kasar Yemen domin zalunci da danniya.