IQNA

Masallacin Damascus Na Daya Daga Cikin Muhimman Wuraren Tarihi

17:31 - April 28, 2016
1
Lambar Labari: 3480361
Bangaren kasa da kasa, babban masallacin Damascus na kasar Syria na daga cikin muhimamn wurare na tarihin msulunci bayan masallacin manzo (SAW) da kuma masallacin Quds.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «CURRENT» cewa, babban masallacin Damascus na kasar Syria an gina shi shekaru 1000 kafin haihuwar annabi Isa (AS), inda al'ummomi daban-daban suka yi ibada a cikinsa, bayan annabi Isa (AS) kuma aka mayar da shi majami'a, da addinin muslunci ya zo kuma aka mayar da shi masallaci,a wannan wuri ne kuma aka bizne kan annabi Yahya (AS) a lokacin da azzaluman mahukunta na lokacinsa suka kashe shi.

Halifofin bani Umayya sun mayar da wannan wuri masallaci karkashin ikonsu, kuma daga lokacin ake kiransa masallacin Bani Umayya.

Daga bisani a cikin karni na hudu na miladiya an samu wani akwati, wanda a cikinsa aka bizne kan annabi Yahya (AS) a cikin wannan masallaci.

Haka nan kuma an gina wasu dogayen hasumiyoyi guda biyu da sunan annabi (AS) a wannan wuri mai dogon tarihi.

Pop John Poul na biyu ya kai ziyara a wannan wuri tun shekara ta 2001, saboda bayanan da ke cewa a nan aka bizne kan annabi Yahya (AS) da kuma annabi (AS).

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
3
innaso insamucekakitarihi masallacei siriyani kum away a finals no
captcha