Kamfanin dillanicn labaran iqn aya
habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Iina cewa,
Abubakar Keita shugaban kasar ta Mali ne zai jagoranci gudanar da zaman taron.
Bayanin ya ci gaba da cewa, run a ranar Juma’a da ta gabata ce aka cimma wannan yarjejeniya ta gudanar da wannan zaman taro a birnmin Bamako, tsakanin mataimakin babban sakataren kungiyar ISESCO da kuma ministan ilimi na kasar Mali.
Wannan shiri dai kungiyar bunkasa harkokin ilimi da ala’adu ta kasashen msuulmi c eke daukar nauyin shirya shi tsawon shekaru kimanin twakwa s ke nan a jere, inda suke tattauna muhimman batutuwa da suka shafi yanayin ilimi da al’adu da suka shafi musulmi.
Yanzu haka dai jami’an kungiyar ta Isesco sun yi rangadi a kasar ta Mali domin duba wuraren da za a gudanar da taron, da kuma wuraren ajiye baki, inda suka nuna gamsuwarsu da shirin da gwamnatin Mali ta yi.
A zaman da ya gudana a shekarun baya an gudaanar da shi a Saudiya, Libya, Kuwait, Azarbaijan, Malaysia, Sudan da kuma Morocco.
Kuma kungiyar tana gudanar da wannan shiri ne karkashin kulawar kungiyar kasashen msuulmi ta duniya.