IQNA

An Bude Masallaci Na Farko A Garin Anapolis Na Kasar Amurka

23:23 - May 09, 2016
Lambar Labari: 3480396
Bangaren kasa da kasa, an bude masallacin Ansar na farko a garin Anapolis na kasar Amurka tare da halartar wasu daga cikin jami’an gwamnati da na tsaro.
Kamfanin dillancin labaran iqn ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Digital Gaztte cewa, an gudanar da bikin bude wannan masallaci a garin na Anapolis wanda muuslmi bas u taba yin irinsa ba.

Wannan taro dai ya samu halartar wasu daga cikin jami’ai na gwamnati da suka hada da jami’an tsaro, kamar yadda kuma wasu daga cikin masu kula da cibiyar muslunci ta yankin suka kasancea wurin.

Samir Islama’il shi ne darakta mai kula da ayyukan masallaci, yabbayana lokacin bude wannan masallaci cewa, sun yi farin ciki matuka da Allah ya basu wannan babbar dama ta gina masallaci na farko a wannan gari, kuma wannan zai bamu damar wayar da kan musulmi domin nisanta su daga duk wani tunani na ta’addanci da ke bata sunan addinin muslunci.

A nasa babban garen babban jami’in yan sanda na garin Anapolis ya samu halartar wurin tare da wasu jami’an yan sanda, inda ya bayyana cewa, halartarsua wannan wuri ba batun tsaro n ekwai ba, har ma suna son su samu masani kan addinin mulunci yadda ya kamata daga bakin musulmi.

3495950

captcha