IQNA

Masani A Amurka: Riskar Ma’anonin Kur’ani Shi Ne Mafita Ga Zamani

21:01 - May 10, 2016
Lambar Labari: 3480399
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Shu’ab Shahid wani masani kan halayyar bil adama a kasar Amurka ya bayyana cewa fahimtar koyarwar kur’ani it ace mafita ga matsalolin zamani.
Kamfanin dillancin labaran Iqnb aya habrta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Pak Obsever cewa, Muhammad Shu’aib Shahid masani kan halayyar dan adam dan kasar Amurka ya bayyana cewa, idan da za a koma ga koyarwar kur’ani da kuma yin amfani da ita, da an samu warware matsaloli da dama na wannan zamani.

Shu’aib ya bayyana hakan ne a cikin wani littafinsa da ya rubuta kan hallayar al’ummomi, inda yabbayana cewa muslunci yana da amsoshi wadanda suke mafita ga matsalolin bil adama.

Ya ce kur’ani mai tsarki shi ne yake dauke da dukkanin wannan koyarwa ga musulmi, kuma idan za ayi nazari ta natsu a cikin darussan da yake koyarwa za a amfana matuka.

Ya bayyana cewa wasu daga cikin msuulmi suna yin amfani da sunan mulsunci wajen cimma wasu manofofinsu na kashin kansu, da hakan kan bata sunan addinin mjslunci a idon duniya.

Daga karshe yay i kira ga musulmi da ma wadanda ba muslmi da su koma zuwa ga kur’ani su yi nazarinsa,kuma su aikata abin da yake umarni da shi, za su samu mafita a cikin rayuwarsu ta duniya.

3496304

captcha