IQNA

An Kori Wata Musulma Sabuwar Muslunta Daga Makaranta A Faransa

21:04 - May 10, 2016
Lambar Labari: 3480400
Bangaren kasa da kasa, an kori wata Daliba musulma daga Makaranta saboda ta sanya dogon hijabi a kasar Faransa
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Independent cewa, daraktan wannan makaranta dake gefen birnin Paris ya shaidawa Dalibar mai shekaru 16 a Duniya, wannan hijabi da ta sanya yana nufin wata alama ta Addini, kuma bisa dokar kasar ta shekara 2014 an haramta amfani da wata alama ta addini a makarantun Gwamnatin kasar.

Bisa dokar kasar Faransa duk wasu kaya da mutum zai sanya ko da dogaye ne babu laifi matukar ba wata alama ba ce ta wani addini.

Ita dai wannan daliba 'yar kasar Portigal ta karfi Addinin islama ne a shekarar 2015 da ta gabata kuma ta gudanar da bincike dangane da alakar yanayin karantarwar Faransa da Addinin Islama.

A shekarar 2004, Gwamnatin kasar Faransa ta haramtawa dukkanicin dalibai musulmai sanya hijabi a cikin Makarantun Gwamnati.

3496412

captcha