IQNA

21:01 - May 11, 2016
Lambar Labari: 3480401

Mataimakin Bankin Moon: Myanmar Na Nuna Banaranci A Kan Musulmi

Bangaren kasa da kasa, Adama Ding mataimakin babban sakataren majalisar dinkin duniya ya ce ana ci gaba da nuna siyasar bangaranci ga mabiya addinin muslunci na kabilar Ruhigya a Myanmar.

Mataimakin Bankin Moon: Myanmar Na Nuna Banaranci A Kan Musulmi
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na Ina cewa, Adama Ding mataimakin babban sakataren majalisar dinkin duniya ya ce ana ci gaba da nuna siyasar bangaranci ga mabiya addinin muslunci na kabilar Ruhigya a kasar Myanmar wanda hakan zai iya kawo kisan kiyashi a kansu.

Ya ci gaba da cewa; da mun kasance muna da fatan ganin cewa idan sabuwar gwamnati ta zo za ta dauki matakin kare marassa rinjaye na kasar yan kabilar Ruhingya, amma abin ban takaici babu abin da ya canja.

Adama Ding y ace idan irin wannan dabi’a ta kabilanci da nuna wariya ga marassa rinjaye ba ta kawo karshe a Myanmar ba, to mai yiwuwa asake ganin wani kisan kiyashi a kasar.

Abin tuni a nan dais hi ne, gwamnatin kasar Myanmar ba ta dauki musulmin kasar yan kabilar Ruhingya a matsayin yan kasa na Sali ba, tana kallonsu a matsayin bakin haure ne da suka shigo kasar ba bias kaida bat un taruruwan shekaru da suka gaba.

Da dama daga cikin masu bin diddigin lamrra sun dauka cewa idan Ang San Sochi ta lashe zabe wadda ta shara wajen kare hakkin bil adama kuma ta samu kyautar nobel to lamurra za su canja, to amma maimakon hakan ma sai lamurran suka kara muni a kan musulmi.

3497208

captcha