IQNA

Mai Gasa Daga Komoros:

Gasar Kur’ani A kasar Iran Babban Darasi Ne Ga Dukkanin Masu Gasa

22:41 - May 13, 2016
Lambar Labari: 3480408
Bangaren kasa da kasa, wakilin Komoros a gasar karatu da hardar kur’ani a Iran ya bayyana cewa wannan gasar darasi ce ga dukkanin masu gasa.
Kamfanin dillancin labaran Iqna daga wurin gudanar da gasar kur’ani ya bayar da rahoton cewa, Ajib Abwan da shekaru 16 wakilin Komoros a gasar karatu da hardar kur’ani karo na 33 a Iran ya bayyana cewa wannan gasar darasi ce ga dukkanin masu halratar wannan gasa ta kur’ani.

Ya ce wannan shi ne karon farko da ya taba zuwa kasar Iran, amma hakika lamarin yay i masa tasiri matuka, domin kuwa yadda jami’ai da masu kula da gasar suka tarbe suka girmama su, abin ya burge atuka.

Haka nan kuma dangane da yadda taron gasar yake gudana ya bayyana gamsuwarsa matuka da irin dukkanin tsare-tsaren da aka yi.

Kamar yadda kuma ya sheda cewa yana halartar bangaren hardar dukkanin kur’ani mai tsarki ne a wannan gasa, kuma yana yin fatan alkhairi ga dukkanin mahlarta gasar da kuma wadanda suka shirya ta kuma suke daukar nauyinta.

Wannan dalibi da ya fito daga tsibirin Komoros dais hi mafi karancin shekaru a tsakanin dukkanin masu halartar wannan gasa daga kasashen ketare.

3497510

captcha