
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora na yanar gizo cewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar imani da Allah da kafircewa wa daguti su ne tushe na hakika na karfi da iko, haka nan kuma yayin da yake jaddada cewa Amurka ita ce babbar dagutu sannan kuma babbar shaidaniya ya bayyana cewar: Babban nauyin da ke wuyan malamai da masana a yau shi ne wayar da kai da bayanin yaudara da kokarin wasa da hankalin al'umma da dawagitai suke yi, sannan kuma wajibi ne su ma al'ummomin kasashen musulmi su yi taka tsantsan kada su fada tarkon yaudarar masu tinkaho da karfi na duniya sannan kuma kada su tsorata da barazanarsu.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da mahalarta gasar karatun Alkur'ani mai girma na kasa da kasa karo na 33 da aka gudanar a birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Haka nan kuma yayin da yake godiya da kuma jinjinawa wadanda suka shirya wannan gasar Alkur'anin, Jagoran ya bayyana Alkur'ani mai girma a matsayin tushen "hadin kan al'ummar musulmi" yana mai cewa: A daidai lokacin da ma'abota girman kai suka tsaya kyam wajen haifar da rarrabuwan kai da rikici tsakanin musulmi, wajibi ne al'ummar musulmi su yi riko da tafarkin hadin kai da fahimtar juna a tsakaninsu suna masu riko da wannan babbar ni'ima ta Ubangiji (Alkur'ani mai girma).
Ayatullah Khamenei ya bayyana debe kewa da Alkur'ani a tsakanin bangarori daban-daban na al'umma musamman matasa a matsayin daya daga cikin albarkokin majalisin karatun Alkur'ani mai girma, daga nan sai ya ce: A halin yanzu dai al'ummar musulmi, sama da lokutan baya, suna bukatar koyarwa da fahimtar ma'anoni na Alkur'ani mai girma. Don kuwa a halin yanzu akwai gagarumar tazara tsakanin rayuwar al'ummar musulmi da koyarwar Alkur'ani.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da gagarumin kokarin da ma'abota girman kan duniya suke yi wajen cutar da Musulunci da al'ummar musulmi, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar: Wadannan mutanen sun san cewa matukar musulmi suka yi karfi, sannan muryoyinsu suka yi karfi da isa ko ina a duniya, to kuwa ba za su sami damar zaluntar sauran al'ummomin duniya ba, sannan kuma ba za a taba mancewa da batun Palastinu a matsayinta na daya daga cikin kasashen musulmi ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana riko da Alkur'ani mai girma a matsayin sirrin nasara a kan wadannan makirce-makirce na makiya da kuma samun hakikanin karfi, daga nan sai ya ce: Karfi na hakika yana cikin imani da Allah da tsayin daka da kuma kafircewa dagutu ne.
Haka nan kuma yayin da yake nuna bakin cikinsa da yadda wasu kasashen musulmi suka rungumi dagutan duniya maimakon riko da Allah Madaukakin Sarki, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Ko shakka babu duk wata kasar da take gudanar da siyasar Amurka a yankin nan, to a hakikanin gaskiya ta ha'inci al'ummar musulmi da kuma share fagen tabbatar da ikon Amurka a yankin nan ne.
Jagoran ya bayyana imani da Allah da tsayin dakan al'ummar Iran wajen tinkarar kokarin wuce gona da iri da mulkin mallakar Amurka a matsayin tushen karfi da tsayin dakan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, daga nan sai ya ce: Dalilin kiyayyar da manyan kasashen duniya suke yi da al'ummar Iran da kuma nau'oi daban-daban na makirce-makircen da suke kulla wa wannan al'umma, ya samo asali ne sakamakon riko da koyarwar Musulunci da suka yi, don kuwa makiya suna tsoron "Musulunci ma'abocin karfi da jaruntaka".
Har ila yau kuma yayin da yake bayyana cewa ayyuka da matsayar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take dauka cikin gaskiya su ne babban dalilin irin tasirin da take da shi a cikin zukatan al'ummar musulmi, kana kuma daya daga cikin dalilan irin karfin da Iran take da shi,, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Ya zuwa yanzu dawagitai sun gaza wajen yaudarar Iran da alkawurransu, haka nan kuma barazanarsu ta gaza wajen razanar da al'ummar Iran.
Ayatullah Khamenei ya bayyana rashin fadawa tarkon alkawurran yaudara na manyan kasashen duniya da kuma rashin tsorata daga barazanarsu a matsayin daya daga cikin manyan bukatun duniyar musulmi. Daga nan sai ya ce: A halin yanzu babban nauyin da ke wuyan dukkanin al'ummar musulmi musamman malamai, masana da ‘yan bokon kasashen musulmi, shi ne tsayin daka da gwagwarmayar wayar da kan al'umma dangane da halin da duniyar musulmi take ciki.
Jagoran ya bayyana bayyanar kungiyoyin ta'addanci ‘yan takfiriyya a yankin nan da kuma haifar da yaki da rikici tsakanin musulmi a madadin makiya a matsayin sakamako na rashin wayar da kan al'umma da bayyana musu hakikanin koyarwar Musulunci. Daga nan sai ya ce: Wajibi ne a yi amfani da majalisin Alkur'ani mai girma wajen wayar da kan al'umma, sannan kuma wajibi ne mutanen da suke halartar irin wadannan tarurruka na Alkur'ani daga kasashe daban-daban, su wayar da kan al'ummomin in sun koma.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da cewa taimakon Allah yana tare da yunkurawar al'umma ne, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Ko shakka babu, lokaci na zuwa da ma'abota kafirci za su rusunawa ma'abota Musulunci na hakika da kuma ja da baya.
Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci sai da Hujjatul Islam wal muslimin Muhammadi, wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci kana kuma shugaban cibiyar lamurran addini na kasar Iran ya gabatar da jawabinsa dangane da gasar karatun Alkur'ani karo na 33 da aka ba shi taken "Littafi Guda, Al'umma Guda" inda ya ce: A yayin wannan gasar, mutane 130 ne da suka fito daga kasahen 70 na duniya suka gudanar da gasar a fannoni daban-daban da suka hada da hadda da kuma karatun Alkur'ani. Kamar yadda kuma yayi Karin haske kan yadda aka gudanar da gasar.