
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na bangaren hulda da jama’a na hubbaren Abul fadl Abbas cewa, a jiya an gudanar da wani taron karatun kur’ani mai tsarki na tarukan sha’aban a tsakanin haramain wato hubbaren Imam Hussain (AS) da hubbaren Abbas (AS), wanda tazara mita 378 ke tsakaninsu.
Wannan taro ya samu halartar fitattun makaranta kur’ani mai tsarki, wadanda suka kawatta wurin da sautinsu da ayoyin kur’ani mai tsarki.
Daga cikin wadanda suka yi karatun kuwa har Hajji Mustafa Sarraf, fitaccen makarancin kur’ani mai tsarki na kasar Iraki, sai kuma Ali hamad Kalkawi, wanda shi ne makarancin kur’ani na hubbaren bbas mai tsarki (AS) sai kuma shi ma Laith Al-ubaidi makarancin kur’ani na kasar ya gabatar da tasa tilawa.
Wannan taro dai ya samu halartar dubban masu ziyara a wannan wuri mai tsarki.
Abin tni a nan dais hi ne, hubbarenAbbas (S) ya jima yana daukar nauyin shirya taruka da suka danganci kur’ani mai tsarki, wanda hakan kumayake samun karbuwa matuka daga masu ziyara da suke zuwa wurin daga kasar dama sauran kasashen na daga masoya Ahlul bait (AS).