
A sakamakon wannan shiri Ibrahim Alafaliqah wanda shi ne ya fara, shi an samu nasarar yaye dalibai masu tarin yawa da suka iya hardace kur’ani mai tsarki ya zuwa yanzu.
Bisa ga yadda tsarin yake gudana, ana dora mutane kan tafarkin hardar kur’ani ne bisa wani tsari na musamamn, wanda idan suka bi shi za su samu damar yin wannan harda a cikin wani kayyayden lokaci.
Sa’ad Turki daya daga cikin mayna jami’an gwamnatin kasar yana daga cikin wadanda suka halrci wurin, kuma ya yaba matuka da yadda wananns hiri yake gudana da kuma irin karbuwar da ya samua wajen jama’a na yankim wadanda abiya mazhabar shi’a ne.
Abin tuni a nan dai shi ne ibrahin Afaliqah daya ne daga cikin fitattun malamai ta fuskar kur’ani a kasar wadanda suka shahara.