Bangaren kasa da kasa, Ahmad Tayyib ya sheda ma jakadun kasashen musulmi a kasar Faransa cewa su zama masu bayyana hakikanin fuskar muslunci ga al’ummomin yammaci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-shuruq cewa, Ahmad Tayyib ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da jakadun na kasashen musulmi a kasar Faransa, da kuma shugaban babbar cibiyar musulmi a kasar kan cewa su zama masu bayyana hakikanin fuskar muslunci ga al’ummomin yammaci maimakon yadda suke kallon muslunci.
Ya ci gaba da cewa babban aikin da ke a gaban musulmi da suke zaune a kasashen turai da ma wasu kasashe da ban a musulmi ba, shi ne su bayyana hakikanin kyakkyawar fuskar muslunci ga al’ummomin wadandannan kasashe.
Ahmad Tayyib ya ce bababr matsalar da ake fama da ita ta ta’addanci a duniya a halin yanzu sanya wasu suna kallon addinin muslunci a matsayin addinin ta’addanci, sakamakon yadda yan ta’adda suke yi ayyukansu da sunan addini.
Shehin malamin ya ce addinin muslunci ba shi da wata alaka da abin da yan ta’adda suke yi, bil hasali ma muslnci ya barranta daga masu yin hakan da kuma masu dauke da irin wannan akida mai bata sunan musulunci da koyarwarsa.
Kamar yadda kuma ya yi ishara da cewa, dole ne masana su mike domin wayar da kan musulmi, musamman ma matasa wadandsa su aka fi sauran yaudara tare da cusa musu mummunan tsatsauran ra’ayi na kafirta sauran musulmi.
Daga karshe ya yi nasiha ga dukkanin mutanen da ya gana da su da cewa su zama masu bayar da kyakkyawan misali kan addinin muslunci, ta yadda za a gane cewa musulmi bas u da wata mummunar kida ta kin sauran al’ummomi ko kyamarsu.