IQNA

Larabawa ‘Yan majalisa A Isra’ila Za Su Salla A Masallacin Aqsa

23:31 - May 28, 2016
Lambar Labari: 3480457
Bangaren kasa da kasa, larabawa yan majalisar keneset ta Isra’ila sn za su salla a cikin masallacin Aqsa a cikin watan Ramadan mai kamawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palastinu cewa, Mas’ud Ganaim daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin Isra’ila ya bayyana cewa a cikin watan Ramadan za su rika yin salla a cikin masallacin Aqsa ne.

Ya ce tun kafin wannan lokacin sun riga sun kudiri a niyar yin hakan, domin kuwaya zuwa kimanin watanni 8 kenan da aka hana su yin salla cikin masallacin Aqsa alkiblar musumi ta farko.

Mas’ud Ganaim y ace sun aike da wata wasika zuwa ga firayi ministan haramtacciyar kasar Isr’ail Ben yamin Netanyahu da kuma Yuli Delstain shugaban majalisar Kenet da kuma Roni sheikh babban jami’in yan sanda na yahudawa kan cewa, a cikin wannan aumin dukkanin yan majalisa larabawa za su rika yin salla a cikin masallacin Aqsa.

Ya ce sun sanar da jami’an gwamnatin ne kawai, amma ba suna neman izni ko karbar umarni ba ne daga gwamnatin yahudawan sahyuniya, domin kuwa ba su bukatr izini domin yin bautar ubangiji.

3501855

captcha