IQNA

Yahudawan Sahyuniya Sun Kutsa A Cikin Hubbaren Annabi Yusuf (AS) A Nablus

16:26 - June 04, 2016
Lambar Labari: 3480477
Bangaren kasa da kasa, kimanin yahudawan sahyuniya 3000 ne suka kutsa kai a cikin hubbaren annabi Yusuf (AS) da ke Nablus a gabar yamma da kogin Jordan a Palastinu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar talabijin ta Almayadeen ta bayar da rahoton cewa kimanin yahudawa 3000 da jijjifin safiya suka kutsa kai a cikin yankin Balata da ke tazarar kilo mita daya daga birnin Nablus a gabashin birnin, tare da rakiyar daruruwan jami'an tsaron Isra'ila da suke ba su kariya a hukumance.

Yahudawan sun shiga wannan wuri mai alfarma wanda a nan kabarin annabin Allah Yusuf (AS) yake domin gudanar da wasu bukukuwansu na yahudawa, wanda musulmin poalastinu ke kallon hakan a matsayin wani mataki na tsokana ga musulmi, domin hakan keta alfarmar wanann wuri ne mai alfarma.

Ko a shekarar bara ma yahudawan sun kai irin wannan kutse a cikin wannan wuri mai alfarma, inda suka keta alfarma ta hanyar gudanar da tarukansu da bukuwan na yahudawa a cikinsa.

3503649

captcha