
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalkto daga shafin jagora cewa, a safiyar yau Lahadi ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaba da 'yan majalisar shawarar Musulunci ta Iran karo na goma inda yayin da yake jaddada wajibcin kiyaye karfi, mutumci da kuma matsayin da majalisar shawarar Musuluncin take da shi cikin gudanar da kasa yayi ishara da wajibcin da ke wuyansu wajen tabbatar da kafa dokoki masu kyau a majalisar. Har ila yau kuma yayin da yake lissafa abubuwan da ya kamata 'yan majalisar su fi ba su muhimmanci a fagagen tattalin arziki na dogaro da kai, al'adu da siyasa ta cikin gida, yanki da kuma kasa da kasa ya bayyana cewar: Wajibi ne majalisar shawarar Musulunci, a kokarin da ake yi na tabbatar da kwanciyar hankali a cikin kasa, ta zamanto mai akidar juyin juya hali da kuma ruhi na juyin juya hali yayin gudanar da aikinta, sannan kuma mai mayar da martani ga matakan kiyayya na Amurka da kuma tsayin daka wajen tinkarar bakaken siyasar ma'abota girman kai.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya fara jawabin nasa ne da taya 'yan majalisar murnar zaban da al'umma suka yi musu a matsayin wakilansu a majalisar dokokin, inda ya bayyana matsayin majalisar a matsayin wani matsayi mai girman gaske yana mai cewa: Nauyin kafa dokoki da ke wuyan majalisar, wani nauyi ne mai muhimmancin gaske. A hakikanin gaskiya ma yana a matsayin share hanya ne ga tafiya da gudanar da ayyukan gwamnati.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da cewa nauyin sanya ido da ke wuyan majalisar koda wasa bai yi hannun riga da batun ba da hadin kai ga gwamnati wajen gudanar da ayyukanta ba, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wannan hadin kai da aiki tare ba yana nufin majalisa ta yi watsi da hakkinta ba ne. A'a, wajibi ne 'yan majalisa su yi aiki da karfin da doka ta ba su wajen gudanar da ayyukansu na bincike da sanya ido wajen ganin an gudanar da dokoki yadda ya dace.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da rantsuwar da 'yan majalisar suka yi na kiyaye tushen koyarwar Musulunci da kuma nasarorin juyin juya halin Musulunci, Jagoran ya bayyana cewar: Wajibi ne majalisa ta zamanto a sahun gaba na gudanar da ayyukan kasa, sannan kuma kiyaye karfi, mutumci da kuma matsayi mai girma da majalisar take da shi yana wuyan 'yan majalisar ne.
Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewa daya daga cikin abubuwan da suke lamunce kiyaye matsayi mai girman gaske na majalisar shawarar Musuluncin shi ne sanya ido kan ayyukanta, Jagoran yayi ishara da batun kafa dokoki masu kyau da kuma wajiban hakan inda ya ce: Wajibi ne dokoki su zamanto, masu kyau, karfi, wadanda suka tabo dukkanin bangarori, wadanda suke a fili, ba tare da sun ci karo da sauran dokoki ba, masu adawa da rashawa da cin hanci, wadanda suka yi daidai da siyasa ta kasa, wadanda suka samo asali daga mahanga ta masana da suke cikin gwamnati da ma wajenta kana kuma wadanda suke la'akari da maslaha da manufofi na kasa ba wai ta kashin kai ba.
Ayatullah Khamenei yayi ishara da kudurin doka ta shida ta ci gaban kasa ta Iran a matsayin daya daga cikin ayyuka masu tsananin muhimmanci na majalisar inda ya ce: Kasar nan tana cikin yanayi ne na musamman. A saboda haka wajibi ne a yi dubi sosai cikin wannan kundin doka don amincewa da ita.
Haka nan yayin da yake ishara da kasantuwar wani adadi mai yawa na sabbin fuskoki a cikin 'yan majalisar, Jagoran ya bayyana cewar: Ni dai ina ganin wannan lamarin a matsayin wata dama, don kuwa kasantuwar wasu sabbin 'yan majalisa a tare da tsoffin hannu, wani lamari ne da zai share fagen samar da wata majalisa ma'abociyar nishadi da ruhin aiki, inda sabbin hannun za su iya amfanuwa da kwarewar da tsoffin hannun suke da ita.