Bangaren kasa da kasa,wasu yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra'ayi sun nemi yin kutse a yau a cikin harabar masallacin Quds mai alfarma, yayin da daruruwan masallata da ke cikin masallacin suka yi musu waigi.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga Anatoli ya bayar da rahoton cewa, Sheikh A'azam Kutaib babban malami da ke kula da harkokin masallacin Quds ya fadi yau cewa, kimanin yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra'ayi 135 suka nemi kutsawa cikin masallacin mai alfarma, amma musulmin da ke cikin masallacin wadanda adadinsu ya kai daruruwa, suka kilace harabar masallacin baki daya, tare da hana yahudawan saka kafa a cikinsa.
Yahudawan wadanda suke samun kariya daga jami'an yan sanda na haramtacciyar gwamnatin Isra'ila, sun janye bayan da suka kasa ture katangar karfen da masallata suka kafa a harabar masallacin.
Yahudawan dai sun kudiri aniyar gudanar da tarukansu ne na idil Tilmud a cikin wannan wuri mai tsarki, lamarin da musulmin palastinu ke kallon hakan a wani mataki na tsokana ga musulmi.