IQNA

19:20 - June 16, 2016
Lambar Labari: 3480521

Sahyuniyawa Sun Yi Na’am Da Matakin Saudiyya Na Hana Iraniyawa Zuwa Haji

Bangaren kasa da kasa, yahudawan sahyuniya na Isra’ila sun yi na’am da matakin da Saudiya ta dauka na hana alhazan Iraniya zuwa aikin hajjin bana.

Sahyuniyawa Sun Yi Na’am Da Matakin Saudiyya Na Hana Iraniyawa Zuwa Haji

Kmafanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alalam cewa, Simantof wani mai sharhi a tashar talabijin ta 10 ta Isra’ila ya bayyana cewa sun yi na’am da matakin da Saudiya ta dauka na hana alhazan Iraniya zuwa aikin hajjin bana kuma hakan ya yi kyau matuka suna frin ciki.

Ya bayyana cewa, a kowace shekara Iraniyawa suna hajji tare yan sunna amma su suna la’antar Amurka da Isra’ila a wajen aikin hajji, wanda bana hakan ba za ta faru ba, kuma hakan abin farin ciki ne ga kowane bayahuden Isra’ila.

Tun kimanin shekarun 20 da suka gabata dai bayn kisan gillar da mahukuntan Saudiyya suka yi alhazn Iran a wurin aikin hajji, ba ataba samun wani tsaiko ba sai wannans hekara.

Mahukuntan Saudiyya dai sun fake da farmakin da wasu Iraniyawa da suka hada da dangin mutann da aka kasha muna suka kai kan karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Mashhad da Tehran, inda ta yanke alaka da Iran baki daya.

3507573

captcha