IQNA

Ranar Quds Ta Duniya Alkawali Ne Na Kare Wuraren Muslunci Masu Tsarki

23:55 - June 29, 2016
Lambar Labari: 3480564
Bangaren kasa da kasa, Kwamitin kawance tsakanin Palastinawa da jamhuriyar muslunci ta Iran ya bayyana ranar Quds ta duniya a mtsayin alkawali ne kare wurare masu tsarki da ke palastinu da kuma goyon bayan wannan al'umma da ke karkashin zaluncin yahudawa.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin cibiyar yada ala'adun muslunci ta jamhuriyar muslunci cewa, a cikin bayanin da kwamitin ya fitar a yau, ya sanar da cewa babbar manufar ranar Quds ta duniya ita ce raya ruhin al'ummar musulmi dangane da kumajin kare wurare masu tsarki a cikin addinin muslunci da ke karkashin mamayar yahudawa a Palastinu, wuri mafi muhimamnci da ke karkashin mamar yahudawan shi ne masallacin Quds mai alfarma.

Bayanin ya ce batun Quds sha'ani na dukkaninal'ummar musulmi ba palastinawa kawai ba, kuma gudanar da tarukan ranar Quds dama jerin gwano gwargwadon yanayin kasashe, yana da bababn tasiri wajen tunatar da al'ummar musulmi wannan lamari mai matukar muhimamnci a gare su.

Kamar yadda kuma hakan yake da tasiri wajen saka yahudawan sahyuniya su zama cikin masani a kan cewa, musulmi suna sane da quds da kuma halin da take ciki, kamar yadda kuma suke da masaniya kan ta'asar da yahudawan ke aikatawa kan wanann wuri mai tsarki.

3511381

captcha