IQNA

21:56 - July 01, 2016
Lambar Labari: 3480571

Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ita Ce Makiya Ta Bai Daya Ga Dukkanin Kasashen Musulmi

Bangaren siyasa, Sayyid Abdulmalik Badruddini Alhusaini Alhuthi ya bayyana haramtacciyar kasar Isra'ila a matsayin makiyi na bai daya ga dukkanin kasashen musulmi.

Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ita Ce Makiya Ta Bai Daya Ga Dukkanin Kasashen Musulmi
Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin Press TV cewa, Abdulmalik Huthi jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabin ranar Quds ta duniya.

Inda ya ce al'ummar palastinu suna cikin kangi na zalunci na tsawon shekaru, wanda wanda kuma wajibi ne da ya rataya akan dukkanin kasashen musulmi da su tsaya tare da al'ummar palastinu wajen nuna musu goyon baya.

Ya ce makiyin al'ummar musulmi guda daya ne shi ne haramtacciyar kasar Isra'ila, duk sauran masu cutar da musulmi suna aiki ne ga Isra'ila da kuma hankoron kare manufarta.

Abdulmalik Huthi ya ce al'ummar Yemen za su ci gaba da tsayawa tare da al'ummar palastinu tare da bas u cikakken goyon baya wajn yaki da suke domin kwatar 'yancinsu daga mamayar yahudawa da kuma kubutar da masallacin Quds da sauran wuraren musulmi masu tsarki.

Wannan jawabi dai ya zo domin karba kiran marigayi Imam Khomeni (RA) wanda ya assasa wannan rana ta ranar Quds ta duniya a jumar karshen kowane watan Ramadan mai alfarma.

3511712

captcha