Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar mabiya addinin muslunci a cikin jahar Alabama ta kirayi mutanen kasar Amurka da su san addinin muslunci ta hanyar karanta kur’ani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na WHNT News cewa, Ala’uddin Bashir jami’in kula da harkokin yada labarai na cibiyar ya ce dukkanin mutane bayin Allah ne.
Ya ce da musulmi da kirista dukkaninsu suna biyayya ne ga Allah kuma duk da banbanci kan mahanga dangane da annbi Isa Almashu (AS) da ke tsakaninsu, amma kuma imani da Allah mahaliccin kowa ya hada su.
Dangane da matsayin musulmi kan abubuwan da suke faruwa kuwa, ya bayyana cewa babu wani addini da aka safkar daga sama da ya zo domin ya cutar da dan adam.
Domin kuwa a cewarsa duk wanda ya cutar da dan adam babu gaira babu sabar, to hakika ya tafka bababn laifi a mahangar dukkanin addininda suka zo daga sama.
Annabi Isa Almasih (AS) ya zo ne domin ya tabbatar da adalci a tsakanin bil adama, kamar yadda shi ma manzon Alah manzon karshe ya zo da irin wannan sako ne tabbatar da adalci da tseratar da dan adama daga halaka.
Ya ce bababn abin da ke da muhimmanci shi ne ya kamata mutane su san addinin muslunci ta hanyar abin da yake rubucea cikin kur’ani ba a bin da was suke aikatawa da sunan muslunci ba, kuma ba za a san kur’ani da abin da ke cikinsa na sako ba har sai an karanta shi.