Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa
ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta
Al'alam rahoton cewa, acikin wannan makon jami'an tsaron masarautar
Bahrain sun kara matsa lamba wajen kai farmaki a kan jama'a da kame malamai da
'yan siyasa gami da masu kare hakkonin bil adama a kasar, sakamakon nuna rashin
amincewa da keta hurumin babban malamin addini na kasar da masarautar ta yi.
A jiya daruruwan jami'an tsaro ne suka kutsa kai a cikin yankin Diraz da kusa da birnin Manama fadar mulkin kasar, wanda kuma nan mahaifar Sheikh Ayatollah Isa Kasim, kuma a nan yake rayuwa, inda yanzu haka dubun-dubatar mutane daga koina cikin kasar sun tare yankin domin tabbatar da kare lafiyarsa daga duk wani yunkurin cutar da si faga jami'an wannan masarauta, amma jami'an tsaron sun fita daga yanki ba shiri, sakamakon fusata jama'a da suka yi.
Masauratar mulkin kama karya ta Bahrain tana ci gaba da daukar wadannan matakai ne duk kuwa da kiraye-kirayen da bangarori na kasa da kasa suke yi mata, kan ta mutunta al'ummar kasarta, musamman babban malamin addini na kasar wanda shi ne ya fi kowa tasiri a cikin zukatan al'ummar kasar, domin ci gaba da cin zarafinsa zai jefa kasar cikin wani hali da ba a san karshensa ba.