IQNA

23:36 - July 23, 2016
Lambar Labari: 3480640

Masarautar Ali-Saud Ta Haramta Wa Maniyyatan Syria Zuwa Aikin Hajji

Bangaren kasa da kasa, Sarakunan masarautar iyalan gidan Saud sun hana musulmi maniyyata daga kasar Syria zuwa aikin bana, ta hanyar hana su izinin shiga kasar (visa) ba tare da bayyana wani dalili na yin hakan ba.

Masarautar Ali-Saud Ta Haramta Wa Maniyyatan Syria Zuwa Aikin Hajji

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na talabijin ta Alalam ta nakalto daga manyan jami'an ma'aikatar alhazai ta kasar Syria cewa, mahukuntan na Saudiyyah sun ki yarda su bayar da izinin shiga ga maniyya na kasar Syria, ba tare da bayar da wani dalili kan hakan ba, amma dai ma'aikatar alhazan ta Syria ta bayyana hakan da cewa ba ya rasa nasaba da dalilai na siyasa, wanda kuma hakan ya saba wa dukkanin kai'idoji na shari'ar musulunci da sunnar manzon Allah.

Yanzu haka dai dubban maniyyata daga kasar sham da suka yi rijistar sunayensu domin safke farali a bana sun yanke tsammaninsu danagane da hakan, sakamakon kin ba su izinin shiga cikin kasar Saudiyya da masarautar iyalan gidan Saud da ke rike da madafun ikon kasar suka yi.

Wannan dai ba shi ne karon farko da wannan masarauta ta iyalan gidan Saud take yin amfani da batun aikin hajji a matsayin wani makami na siyasa ba, domin kuwa ko a lokacin mulkin Jamal a masar ta haramta wa Misrawa zuwa aikin hajji.

Kamar yadda ta haramta wa al'ummar udan zuwa hajjia lokacin da suka samu sanbanin siyasa da albashir, haka nan kuma sun taba hana al'ummar ibya zuwa aikin hajji sakamakon sabaninsu da mahukuntna kasar.

3516777

captcha