Kamfanin dillancin labaran iqna ya
habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almisrawi cewa,
tsawon wannan kur’ani baki daya bai fi CM4.1 b, kuma shi ne ya zuwa yanzu mafi
karantar kur’ani rubutun hannu.
Shugaban cibiyar da ke kula da harkokin adana kayan tarihi a kasar Yemen ya bayyana cewa, wannan kur’ani ya jima a hannun wannan cibiya, kuma an same shi ne akasar.
Ya kara da cewa har yanzu ba za a iya tntance ko zuwa wane mutum ne wannan kur’ani ke komawa ba, amma dai abin da aka tabbatar da cewa shi ne kur’ani rubutn hannu mafi karanta a duniya a halin yanzu, duk da tsawon shearunsa.
Dangane da yadda ake kula da shi kuma ya bayyana cewa, domin kada takardunsa su lalace, ana kula da shi yadda ya kamata a cikin tsawon wadannan daruruwan shekaru.
Yanzu haka dai za a iya ganin kur’anin da shafukansa da kuma rubutnsa ba tare da wata matsala ba, kamar yadda har yanzu takardunsa na asaline har da bangyensa.