IQNA

23:20 - August 02, 2016
Lambar Labari: 3480671

Halbawi Ya Bayar Da Bayani Da Dalilan Hana Shi Fita Daga Masar Zuwa Iran

Bangaren kasa da kasa, Kamal Halbawi daya daga cikin fitattun masana daga kasar Masar ya bayyana dalilan da suka hana shi halartar wani taro da aka shirya a Iran.

Halbawi Ya Bayar Da Bayani Da Dalilan Hana Shi Fita Daga Masar Zuwa Iran

Bangaren kasa da kasa «gulfeyes.net» Kamal Halbawi daya daga cikin fitattun masana a Masar kuma tsohon mamba a kungiyar yan uwa muslmi ya bayyana dalilan da suka hana shi halartar wani taro da aka shirya a Iran da suke da dangataka da tsaro a kasar ta Masar.

A lokacin da yake zantawa da wasu kafofin yada labarai na Masar Halbawio ya bayyana cewa, bas hi da masani kan cewa akwai wasu kasashe da idan za ka je sai ka yi wasu cike-cike a wajen jami’an tsaro, kuma daga ciki har da Iran, a kan haka ne ya samu jinkirin da ya hana shi halartar taron.

An shirya cewa a ranar Lahadin da ta gabata ce Halbawi zai bar birnin Alkahira zuwa Doha, daga na kuma zuwa Tehran, amma jami’an tsaron kasar Masar sun hana shi fita daga filin safkar jirage na Alkahira.

Ya kara da cewa yana neman uzuri matuka saboda abin da ya faru, domin kuwa an shirya zai gabatar da lacca ne a zaman karshe na taron da ma’aikatar shari’a ta kasar Iran ta shirya.

3519467

captcha