Kamfanin dillancin labaran Kur'ani
na Iqna ya nakalto daga shafin Bawaba News cewa, furuncin da paparoma Francis
ya yi da ke nisanta addinin muslunci daga duk wani aiki ta'addanci ya samu
karbuwa daga cibiyar Azhar da cibiyoyin muslunci.
Paparoma Francis a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a jiya, ya bayyana cewa, babu wata alaka a tsakanin addinin muslunci da abin da wasu suke yi suna dangata shi da addinin muslunci na ayyukan ta'addanci.
Ya ci gaba da cewa a lokacin da shugaban Azahar ya ziyarce a kwanakin baya sun tattauna muhimamn batutuwa da suka shafi ayyukan ta'addanci da tsatsauran ra'ayi daga bangarori biyu, da kuma yadda za a fuskanci hakan domin samun zaman lafiya da fahimtar juna.
Kamra yadda kuma ya bayyana cewa ana ci gaba da tuntubar juna tsakanin cibiyoyin muslunci da kiristanci domin kara karfafa alaka da fahimtar juna da kuma kusanto da al'ummoin biyu.
Daga cikin abubuwan da aka cimmawa a dai akwanakin baya tsakanin Paparoma da kuma babban malamin cibiyar Azahar, har da shirya taruka lokaci zuwa lokaci domin yin bayani kan muhimman abubuwa da suka hada mabiya addinain biyu.
Wannan dai bas hi ne karon farko da babban malamin majami'ar ta Kaltholic yake kare addinin muslunci tare da nisanta shi daga ayyukan 'yan ta'adda ba, inda har yakan buga misali da yadda musulmi suka fi kowa zama ragunan layya a wajen 'yan ta'adda fiye da kiristoci da ma mabiyan wasu addinai.