IQNA

'Yan Ghana Za Su Halarci Taro Kan Imam Ridha (AS)

23:41 - August 09, 2016
Lambar Labari: 3480692
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin masu gudanar da ayyukan yada koyarwar iyalan gidan amnzo daga kasar Ghana za su halarci taro kan Imam Ridha a Iran.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na cibyar yada al'adun muslunci cewa, a jiya wasu daga cikin masu kokarin yada koyarwar iyalan gidan amnzo sun halarci karamin ofishin jakadancin Iran a Ghana, domin tattauna batun tafiyarsu zuwa halartar taron Imam Ridha (AS).

Muhammad Hassan Ipechki ne shuagaban karamin ofishin jakadancin Iran a kasar ta Ghana, ya kuma tattauna tare da su dangane da tafiyar tasu zuwa halartar wanann taro.

A kasar dai akwai makarantu na yada koyarwar makarantar iyalan gidan manzo na Ahlul bait (AS) inda wasu daga cikin mutanen kasar da kuma wasu malamai daga kasar Iran suke koyarwa.

A yau ne dai ake sa ran wanann tawaga ta mutanen Ghana za ta iso kasar Iran domin halartar wanann taro wanda shi ne karo na goma sha hudu da ak egudanar da shi, tare da halartar baki 'yan kasashen waje da dama.

Wannan taro na Imam Ridha (AS) a kowane lokaci ana gudanar da shi ne da nufin fitar da ilmomi da suke kunshe a cikin tarihin rayuwar wannan Imai daga limaman shiriya na iyalan gidan ma'aiki tsira da amincin Allah su tabbataa gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.

Abdulrahim Bangado malami a makarantar Ahlul bait (AS) a Akra da kuma Mahmud Ibrahim Tusi, da kuma Muhamamd Bello wani malami a birnin duk suna daga cikin wadanda za su halarci wannan taro kan Iamm Ridha (AS).

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna%2c
captcha