Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga jaridar Wshington Post cewa, kisan malamin kirista a kasar Faransa ya zo ne daidai lokacin da ‘yan ta’addan Shabab suka kasha gomman musulmi a Magadishou, amma kisan musulmi ba a ambatarsa akafofin yada labarai.
Baynain ya ci gaba da cewa rashin adalci ne na kafofin yada labaran kasashen yammacion turai, yadda suke ta kokarin bayyana ayyukan ta’addanci a matsayin lamari da ke da dangantaka da msuulmi, alhali kuwa musulmin su ne suka dandana kudarsu a hannun ‘yan ta’addan.
Ko shakka babu Faransa tana da banbanci da kasar Somalia ta fuskar ci gaba, da kuma yadda ake kallon matsayin dan adam a matsayinsa na mutum a cikin kasashen biyu, wanda hakan abin ban takaici ne a wannan zamani.
Wannan yan adaya daga cikin abubuwan da dan ta;karar shugabancin Amurka Donald Trump yake ta kamfe da shi, wajen hankoronsa na yada kyamar musulmia cikin kasar Amurka, wanda kuma hakika yana tasiri ga wasu wadanda suke da karancin sanin inda duniya ta nufa.
A cikin shekara ta 2006 Shabab ta samu damar mamaye wasu yankuna a cikin birnin Magadishou na Somalia, kamar yadda kuma a cikin shekara ta 2011 ta kara fadada ikonta akudancin kasar, amma kuma ta samu koma baya a lokacin da dakarun Uganda da Kenya suka shigo cikin kasar.
An kafa wannan kungiya ne bayan matsalolin da Somalia ta shiga tun bayan faduwar gwamnati a cikin shekara ta 1991, bayan ‘yan shekaru kungiyar ta ta’addanci ta Shabab ta bayyana a kasar, wadda ta ginu kan akida ta wahabiyanci, wadda kuma gwamntin Saudiyyah ke daukar nauyinta.