IQNA

Shirin Yahdawa Na Rusa Masallacin Aksa A Cikin Shekaru Uku Masu Zuwa

23:48 - August 16, 2016
Lambar Labari: 3480716
Bangaren kasa da kasa, Mahir Khadir daya daga cikin malaman Palastinawa ya bayyana cewa yahudawa sahyuniya suna shirin rusa masallacin quds a cikin ‘yan shekaru masu.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto dag shafin sadarwa na yanar gizo na Yaum Sabi cewa, a jiya ne Mahir Khadir babban alkalin kotun Palastinawa da ke birnin Quds kuma daya daga cikin ammbobin majalisar malaman Palastinu ya fitar da wani bayani, wanda a cikinsa ya fallasa wani boyayyen shiri da yahudawan sahyuniya suke da shi na rusa masallacin Aksa acikin shekaru 3 masu zuwa.

Ya ce ya aike da wasika zuwa ga kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da kuma cibiyar addini ta Azahar da ke Masar, tare da yi musu bayani dalla-dalla kan shirin, tare da neman su dauki mataki na ganin an taka wa yahudawan birki kan wannan mummunar manufa tasu a kan alkiblar msuulmi ta farko.

Bisa wannan bayanin, yahudawan suna da shirin gina wani babban wurin bautarsu a daidai nda masallacin quds yake, kuma sun fara yada hakan a tsakanin yahudawa domin dasa wannan akidar a cikin zukatansu,inda yanzu haka sun fara daukar matakai na share fagen yin hakan.

Daga cikin irin matakan da yahudawan suke dauka kuwa, har da kai farmaki kusan a kowace rana a kan masallaci, tare da cin zarafin masallata, da kuma gudanar da wasu al’adu na yahudawa a cikin harabar masallacin mai tsarki, kuma suna yin hakan ne tare da rakiyar jami’an tsaron Isra’ila da suke ba su kariya, tare da halartar ‘yan jarida, domin tabbatr wa duniya halascina bin da suke yi a hukumance,a matsayi na cikin gida da kuma a mataki na duniya, domin kuwa babu wani abu da ya taba fitowa daga Majalisar dinkin duniya da ke yin Allawadai da hakan, ko kuma bayyana rashin halascin haka.

3523245

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna palastinawa
captcha