Bayanin ya ci gaba da cewa bisa la’akari da matsayin wannan masalalci a a cikin addinin muslunci da kuam tarihinsa, hakan ya sanya dole ne a rika tunawa da shi, musaman yadda Allah madaukakin sarki ya abaci wannan wuri, da kuma batun tafiyar manzo zuwa masallacin daga nan kuma aka yi tafiya da shi zuwa sama, wanda hakan ya kara tabbatar da matsayin wannan wuri da kuma kasantuwarsa kiblar musulmi ta farko.
Za arika wattsa shirin ne daga ranar Litinin mai zuwa tsawon sa’oi uku a kai tsaye, daga karfe 20 zuwa karfe 22.
Haka nan kuma wannan gidan radiyo yana da wani shirin na musamman wanda a kinsa za a rika jin ra’ayoyin mutanen Palastinu kai tsaye ta hanyar wayar tarho, inda za su rika bayyana halin da suke ciki da kuma abubwan da suke faruwa da su.
Babbar manufar kafa gidan radiyon ita ce kara tunatar da mabiya addinin musulunci matsayin masallacin Aqsa mai alfarma.