Yahudawan sun kai farmakin ne a daidai lokacin da jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila suke ba su kariya, tare da makamai da motoci amsu sulke, domin hana Palastinawa daukar duk wani mataki a kan yahudawan a lokacin da suke cikin masalacin mai alfarma.
Wannan dai ba shi ne karon farko da yahudawan sahyuniya ke yin hakan ba, inda a 'yan watannin baya ma sun lakadawa daruruwan masallata duka a lokacin da suke cikin masalalci, tare da jikkata wasu wasu.
Wannan yana faruwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin manyan kasashen larabawa suke mayar da kyakyawar hulda da haramtacciyar kasar Isra'ila, tare da gayyatarsu zuwa yake-yaken da suke a kan 'yan uwansu larabawa.